Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar idan aka zabe shi shugaban Najeriya a 2023.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin Keffi, Dakta Shehu Chindo Yamusa III ziyara a fadarsa da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.
KARANTA ANAN: 2023: Wasu Magoya Bayan Ka Makiya Ne, Obasanjo Ya Gargadi Tinubu
Jaridar Dimokradiyya ta rawaito cewa Kwankwason ya ce ziyarar da ya kaiwa sarkin ta zama wajibi saboda girmama masarautun da daukacin mutanen garin Keffi.
Da yake yabawa Kwankwaso bisa ziyarar, Sarkin Yamusa III ya yi masa fatan Alheri da kuma Allah Ya saka masa da alheri.
Sanata Kwankwaso dai guda ne cikin masu zawarcin kujerar shugaban kasar Najeriya, a babban zaben 2023 dake tafe.
A wani labarin Kuma: PDP ta caccaki APC kan kiran data yi na tsige gwamnan Arewa
Jam’iyyar PDP ta caccaki APC kan kiran da jam’iyyar ta yi na a tsige Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe, Vanguard ta rawaito.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Mista Danial Ihomun a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai kwanakin baya a Makurdi ya yi kira da a tsige Gwamna Ortom bisa zarginsa da kin tabbatar da an gudanar da zaben kananan hukumomi cikin gaskiya da adalci a jihar; ya kuma yi ikirarin cewa ya yi wa kananan hukumomin jihar ba daidai ba.