Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, zai gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a Fatakwal da yammacin yau a ci gaba da neman wanda zai tsaya takara tare da shi a zaben 2023.
Kwankwaso dai ya dade yana tattaunawa da Peter Obi na jam’iyyar Labour domin nazarin yiwuwar hadewar jam’iyyun biyu ko kulla kawance a zaben.
Sai dai ana kyautata zaton cewa tattaunawar ta yi tsami, musamman ma batun da ke cewa tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar biyu, wane ne zai dacewa domin ya zama mataimakin daya.
Ganawar da Kwankwaso zai yi da Mista Wike na iya zama manuniya cewa tsohon gwamnan jihar Kano yana neman wasu hanyoyi don tsira a siyasar.
Mataimakan Kwankwaso da Wike sun tabbatar da cewa ‘yan siyasar biyu sun shirya haduwa a Fatakwal da misalin karfe 2:30 na rana a yau juma’a.
Bangarorin biyu sun kuma ce tattaunawa tsakanin ‘yan siyasar za ta mayar da hankali ne kan zaben shugaban kasa na 2023.
Su biyun dai sun ci gaba da tuntubar juna tun bayan da Kwankwaso ya fice daga PDP.
Idan dai za a iya tunawa, dan takarar jam’iyyar NNPP ya taimaka wa Mista Wike wajen samun kuri’u masu yawa daga wakilan Kano a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a watan jiya.
Wasu jiga-jigan tsohon gwamnan ne ke rike da shugabancin jam’iyyar PDP a Kano, duk da sauya shekarsa da dimbin magoya bayansa daga jam’iyyar.
Sai dai ba a san ko za a shawo kan Mista Wike ya fice daga PDP shi ma ya zama abokin takarar Mista Kwankwaso ba.