Yan kwana -kwana daga Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara sun kawar da gawar wata mata da ba a san ko wacece ba, a kusa da kogin Asa dake garin Ilorin, babban birnin jihar.
Kwanaki uku ke nan bayan da aka gano gawar matar daga rijiya kuma a cikin garin Ilorin.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen da ke zaune kusa da kogin Asa da masu wucewa ta hanyar, sun sanar da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar, lokacin da suka ga gawar marrigayiyar tana yawo a saman kogin.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Hassan Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin, a yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Ilorin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babu Kamshin Gaskiya a maganar kama Uwargidan Gwamnan Kano
Inda ya ce: “An gudanar da wannan aikin Ciro matar ne da misalin karfe 07:48 na safiyar yau talata, a Kogin Asa da ke kan hanyar Emirs na Ilorin a cikin jihar Kwara, bayan da mutanen da ke kusa yankin, suka lura da gawar mutum tana yawo a cikin kogin”
“A halin yanzu, ba a san wacce ta mutu ba, amma an mika ta ga rundunar‘ yan sandan Nigeria reshen jihar Kwara.” A cewar shi.
Kazalika Adekunle ya bukaci sauran Al’uma Baki daya, “da su kasance masu taka tsantsan, don hana faruwar hakan nan gaba.”
Comments 1