By Ishaq Dabai
Gwamnatin jihar Kwara a ranar Lahadin data gabata tace ta bada umurnin a kafa kwamitin bincike don gudanar da bincike kan makarantar Larabci ta Misbaudeen al islamiy Ganmo, a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
An ga wasu ɗaliban makarantar a wani faifan bidiyo ana azabtar da su bisa zargin aikata ayyukan da aka ɗauka cewa sun saɓa wa dokokin makarantar.Gwamnati ta kuma nemi shugaban makarantar larabci, wanda ya yarda ya jagoranci hukuncin, daya ja da baya har sai an kammala bincike.
An ga wasu ɗaliban makarantar maza da mata a cikin faifan bidiyon da aka nada ana bugun su saboda sun je “Club House” don murnar zagayowar ranar haihuwar ɗaya daga cikin abokan karatun su, tare da shaye -shayen barasa, sabanin umarnin addinin Musulunci.
Amma gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi da cigaban jari hujja, Hajiya Sa’adatu Modibbo-Kawu, tace wata tawaga ta ziyarci makarantar, yayin da daliban da abin ya shafa suma an kai su wani asibitin gwamnati domin yi musu magani.
Kazalika Sanarwar ta karanta wani bangare, “Tawagar ta kunshi kwamishinan ilimi da ci gaban jari -hujja, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu; Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Addini (Musulunci) Alhaji Danmaigoro; Dr Saudat AbduBaqi na Jami’ar Ilorin; Mallam Lawal Olohungbebe na Jami’ar Jihar Kwara, da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Rafiu Ajakaye.
“Jami’in‘ yan sandan yanki Ganmo, SP Oko Nkama, da wakilin NSCDC DSC Parati AbdulHameed.”Gwamnati ta kuma kai daliban da abin ya shafa zuwa asibitin gwamnati domin duba lafiyarsu da kula da lafiyarsu.don tabbatar da cewa babu ɗayansu da ke fama da lalacewar jiki ko ta hankali. ”