By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane uku da ake zargin barayi ne da kuma wasu mutane biyu da ake zargin masu karbar kayan sata ne a Ilorin babban birnin jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, Mista Okasanmi Ajayi, ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Ilori, inda yace sunayen wadanda ake zargin sun hada da Ayo Rasaki Sakiru, Iliyasu Rasaki da Jimoh Mashood.
DUBA WANNAN LABARIN: Filato: Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Ne Sun Hallaka Jami’in Soji Da Wasu Mutane Biyu
Ya ce kama wadanda ake zargin ya biyo bayan rahotannin baya-bayan nan na fasa shaguna da sata a wasu unguwanni a cikin birnin Ilorin.
A cewar kakakin, kwamishinan ‘yan sandan, Tuesday Assayomo, ya bayar da umarnin gudanar da tattaki ga DPO na yankunan da lamarin ya shafa da su tashi tsaye domin dakile wannan dabi’a da ta kunno kai tare da tabbatar da cafke duk wadanda suka aikata wannan aika-aika.
“Sakamakon umarnin CP, DPOs sun shiga daukar mataki inda aka kama wadanda ake zargin,” in ji shi.
Okasanmi ya ce “dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma sun bayyana cewa sun fasa shaguna da dama a unguwar Fate da titin Stadium a Ilorin tare da sace wasu kayayyaki masu daraja a ciki.”
Kakakin ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa an kama wata mai suna Fatima Shuaibu ‘f’ da Olajumoke Yusuf ‘f’ wadanda ake zargi da karba da kuma kula da kayayyakin da aka sace.
A karshe dai binciken da aka gudanar ya kai ga kwato wasu na’urorin sanyaya ruwa, injinan wutar lantarki na Elepaq guda hudu, takalma guda shida, kayan Ankara guda 90, babur din Bajaj daya mai dauke da lambar: DPG-589 OGUN da injin Haque Lucky lady daya mai dauke da lambar: KSF. 550 GP.
Sannan Okasanmi ya kara da cewa, “Ana ci gaba da kokarin kama wasu ‘yan kungiyar da kuma yiwuwar dawo da kayayyakin da aka sace.”
Kwamishinan ‘yan sandan, ya sake gargadin masu aikata laifuka da su bar jihar Kwara su koma wani wurin, inda ya bayyana cewa mai laifin da ya yi nasarar aikata laifuka ba zai taba samun nasarar tserewa kamawa ba.
Assayomo ya shawarci duk wani mutum mai ra’ayin aikata laifuka ko ƙungiyoyi don amfanin kansu, da su nisanta kansu daga mugayen hanyoyinsu kuma su rungumi bin doka.
Wadanda ake zargin da aka kama a cikin lamarin nan take da sauran su, za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Comments 1