Wakilinmu Uzairu Dauda Bauchi
Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, ya bada ummarnin kammala aikin gadar Gwaram data lalace a karamar hukumar Alkaleri cikin wata guda.
Gwamnan ya bada ummarnin ne, lokacin da ya jagoranci tawagar jami’an gwamnatinsa don duba gadar data fadi a yankin, sai ya Kara ummartar Sakataren gwamnati da babban Sakataren ma’aikatar ayyyuka dasu tabbatar da Dan kwangilar da aka bashi gyaran gadar ya kammala cikin wa’adin da aka yanke.
Gwamna Abdulkadir Muhammad yace ya bada ummarnin ne don daukar matakin gaggawar ragewa mutanen yankin wahalhalun rayuwa da suke ciki.
Cikin jawabinsa babban Sakataren ma’aikatar ayyyuka, Injiniya Stephen Abubakar wanda ya bayyana ambaliyar ruwa da akayi a Matsayin Ummul aba’isin karyawar gadar, yace za a Kara fadada gadar don biyan bukatun Al’ummar yankin.
Game da hakan, Gwamna Bala Muhammad, ya jajantawa wadanda waki’ar ambaliyar ta shafa a Bakin Kogin, dake yankin Pali karamar hukumar Alkaleri sai ya tabbatar musu da aniyar gwamnati na agajin gaggawa.
Gwamnan yace zai umarci tawagar kwararru domin kaiwa ziyarar duba muhalli a yankin da zummar taimakawa don dakile aukuwar annobar anan gaba.
Tunda farko wani mazaunin garin na Bakin Kogi, ya shaidawa Gwamnan cewa annobar ambaliyar ta shafi gidaje 17 da sauran yankuna a yankin.