A sanyin safiyar Jiya Asabar ne aka ruwaito jami’an tsaro a Jihar Rivers karkashin Limancin Yan sanda suna gadin sakatariyar jam’iyar PDP inda daga bisa wasu mutane suka sauya mishi fenti zuwa na APC.
Cikin wani sako da PDP ta fitar ta ce babu makawa wannan danne hakki ne wanda kuma gwamnan Jihar Ben Ayade ne ya bada damar yin haka, a cewr ta.
Shugaban Kwamitin riko na PDP a jihar ya ce jam’iyyar na da cikakken rasiti na hayan gurin amma dukda haka aka kore su wanda a cewarsa tauye hakki ne.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar Rivas ya gargadi jama’a da kada wani ya kuskura ya yi yunkurin wargaza matakin garambawul wa sakatariyar.
A bangaren jam’iyyar APC kuwa gwamnan ya ce a matsayinsa na jigon PDP a baya wanda yanzu ya sauya sheka zuwa APC yana da hurumin yin hakan.