Hukumar fasa kauri ta ce ta kama Kwantena 53 makare da kwayoyin tramadol da gurbatacciyar shinkafa da kudinsu ya wuce naira bilyan biyu da aka shigar kasar daga Ghana da China.
Shugaban hukumar yaki da fasa kwauri ta Nijeriya, Kanal Hamid Ali ya ce shinkafar dai wadda aka kama ta a birnin Legas ta lalace amma duk da haka wasu ‘yan kasuwa sun sauya wa shinkafar buhu domin nuna cewa shinkafar ta Nijeriya ce.
Wannan dai shi ne wani kame mafi girma mai yawan kwantainoni 53 da aka kama bayan rufe iyakokin Nijeriya.
Kame na farko dai ya zo da hukumar fasa kwauri mai kula da iyakokin Oyo da Osun ta yi ta tabar wiwi ta kimanin miliyan dari.
Gwamnatin tarayya dai ta karyata rahotannin da ke cewa rufe bakin iyakar ya tona asirin Niajeriya cewa yawan shinkafar da take nomawa ba ta isa ta ciyar da ‘yan kasar ba har a sayar ga kasashen da ake makwabtaka da su ba.
Daga karshe Kanal Hamid Ali ya kara da cewa sun samu rahotannin da ke cewar kasar Benin ta yi odar shinkafa daga Japan ta kimanin dala miliyan $32,000,000, domin shigar da ita Nijeriya.