Hukumar Kula da Hana Fasa Ƙwauri ta Najeriya ta tara kimanin Naira Tiriliyan 2,240,880,308,195.77 a shekarar 2021, wanda ya wuce adadin da aka ƙiyasta na Naira Tiriliyan 1,678,715,016,014.00 a shekarar.
KARANTA WANNAN LABARIN:;Edward Egbuka Ya Zama Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kogi Na 36
Haka zalika, Hukumar ta tara fiye da Naira Tiriliyan 1,562,115,419,216.32 a shekarar 2020 wanda ya bayyana ƙaruwar kashi 43.45.
Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam na Ƙasa Hameed Ali ya bayyana cewa wannan nasarar an cimma ta sakamakon buƙatar kula da matsalolin da Lafiyar Al’umma da aka samu matsala, a dalilin cutar Covid-19.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da Jama’a na Kwanturola-Janar Compt. Joseph O. Attah ya fitar.
Sanarwar tace”yanayin kuɗaɗen da ake tattarawa suna cigaba da ƙaruwa duk shekara, a yayinda ake cigaba da yin canje-canje, da sanya jami’ai Da zasu iya aiki akan doka da sauran su.