Makarantar dake horas da jami’an hulda da jama’a ta Nijeriya, wato NIPR a takaice ta yi alkawarin hada guiwa da kawarta na kasar Afrika ta Kudu domin tabbatar da an kawo karshen kyamar baki a kasar Afrika ta Kudu.
Malam Mukhtar Sirajo, shugaban NIPR din ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin ganawarsa da manema labarai a birnin tarayya Abuja. Sirajo ya ce wannan matakin ya zama dole domin ganin an samar da hanya wacce ta dace a tsakanin kasashen biyu wajen kawo karshen kashe ‘yan Nijeriya da tarwatsa dukiyoyinsu a kasar Afrika ta Kudu.
Ya jaddada cewa; komai ya shafi Nijeriya kamar ya shafi Afrika ne baki daya, kamar kuma ya shafi dukkanin wani bakin fata a fadin duniya, duba da yadda Nijeriya ta zama uwa a matsayin kasar da ta fi kowacce a Afrika yawan al’umma da girman tattalin arziki.
Sirajo ya nuna damuwarsa bisa yadda wuraren kasuwancin Afrika ta Kudu dake sauran kasashen Afrika ke fuskantar barazana a wani mataki na maida martani ga abin da yake faruwa ga baki a kasar Afrika ta Kudu din. Ya shawarci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu, sannan su bar gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan kasar Afrika ta Kudu.