Shugaban Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya aiko tawagar jakadu uku zuwa Nijeriya domin neman gafara da sasanci tare da bada hakuri bisa hare-haren da ‘yan kasar sa suka rika kai wa ‘yan Nijeriya tare da sauran baki da ke kasar Afrika ta Kudu, inda ma suka kashe wasu tare da barnata dukiyoyinsu.
Jakadan zai kara jaddada wa Najeriya bukatar kada dankon hadin kai tsakanin kasashen Afrika, tare da tattauna hanyoyin da za a sake tabbatar da zaman lumana a tsakanin kasashen biyu.
An ruwaito cewa Kakakin Shugaba Ramaphosa mai suna Khusela Diko a ranar Lahadi ya na cewa “jakadun uku za su fara kai ziyara Nijeriya sannan su karasa wasu kasashen Afrika shida.”
Ya ci gaba da cewa za su isar da sakon Shugaba Ramaphosa dangane hare-haren da aka kai wa ‘yan wadannan kasashe da ke zaune a Afrika ta Kudu da kuma lalata musu dukiyoyi da aka yi. Sannan kuma za su kara jaddada matsayar Afrika Ta Kudu wajen bin doka da oda.