Gwamnatin Bangladash ta ce ‘yan kasar sama da 400 aka kashe a Afirka ta Kudu, a cikin shekara 4 da suka gabata, sakamakon hare-haren da ake kai wa baki ‘yan kasashen waje. Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da mayar da hankali kan hare-haren da ake kai wa baki ‘yan kasashen waje a Afirka ta Kudu, gwamnatin Bangladesh ta fitar da alkaluman da ke nuna cewar, ‘yan kasar ta 452 aka kashe daga shekarar 2015 zuwa yanzu.
Jakadan Bangladesh a Afirka ta Kudu, Shabbir Ahmad Chowdhry ya ce a cikin wannan shekara kadai ‘yan kasar 88 aka kwashi gawar su zuwa gida, yayin da ake bizne wasu ba tare da an shaidawa ofishinsa ba. Chowdhry ya ce akasarin wadanda aka kashe, an hallaka su ne ta hanyar harbi da bindiga a shagunan su ko kuma kisan gilla sakamakon rikicin kasuwanci ko rigima kan kudade ko kuma alaka da mata.
Ganin yadda aikata laifuffuka ya yi kamari a Afirka ta Kudu, jami’in ya ce wasu ‘yan kasar sa kan yi hayar ‘yan bindiga su hallaka abokan rikicin su. Abdul Awal Tansen, daya daag cikin shugabannin ‘yan Bangladesh mazauna kasar ya ce akwai mutanen su da dama da aka kashe ba tare da sun kai kara ba, saboda ba su da takardun zama. ‘Yan kasar Bangladesh sun fara hijira zuwa Afirka ta kudu ne a shekara ta 2000, kuma yanzu haka adadin su ya kai 300,000.