Shugaban Kamfanin Mai na Kasa NNPC Mele Kyari, ya kalubalanci Matasa kan Gaza amfani da sabbin hanyoyin zamani na kirkira wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Nan.
Kyari ya bayyana hakan a Abuja, yayin da wata kungiya ta shirya taro na musamman ga Matasan, Kan yadda zasu iya bayar da gudunmawa wajen ciyar da tattalin arzikin Nan gaba.
Ya ce a dai dai lokacin da hankalin Gwamnati ya karkata ga bangaren habbaka sinadarin Gas, Kamata yayi Matasa su amfana da hakan ta fuskar sabbin dabaru da akan fitar da su, domin aiki da su a aikace.
Ya Kara da cewa Matasa na damar Sanya hannun jarinsu Kan harkar Gas, da kuma Fetur, dai dai lokacin da ake amfani dangas din wajen samun Hasken Lantarki.