By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin Olu na Warri, Ogiame Atuwatse III, da matarsa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Babban Sarkin Itsekiri ya sanar da ziyarar ne ta wata sanarwa a shafinsa na Instagram mai taken, ‘Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Olu of Want zuwa liyafa a Aso Rock.
Da yake bayar da cikakkun bayanai kan ziyarar, sanarwar ta ce, “A yayin ziyarar, mai martaba ya bayyana wannan ajandar da za ta hada da mai da hankali sosai kan ci gaban matasa ta hanyar samar da sana’o’i da kuma gaggauta samar da damammaki ta hanyar farfado da kadarorin Gwamnatin Tarayya kamar tituna, tashoshin ruwa da muhimman manufofin goyon baya a cikin Masarautar Warri.
“Bayan sun bar shugaban kasa ne, tawagar masarautar ta ci gaba da ziyartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ofisoshi kuma sun kara samun kyakkyawar alaka da shi.
“Mai martaba ya samu rakiyar Mai Martaba Olori Atuwatse III da wasu sarakunan masarautar Want da suka hada da Cif Mene Brown, Cif Oma Eyewuoma, Cif Thomas Ereyetomi, Daniel Reyeneju, Dakta (Mrs) Dere Awosika da Mista Julius Rone, sanannen ɗan kasuwan Itsekiri Oil & Gas wanda ke bada tallafi da gogewa ga cibiyar tunani mai ƙarfi na Mai Martaba.”