By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya isa jihar Kaduna domin gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki biyu.
Shugaban ya taso ne daga birnin Banjul na kasar Gambia inda ya halarci bikin rantsar da shugaba Adama Barrow a karo na biyu.
Gwamna Nasir El-Rufai da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi shugaba Buhari.
Ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin El-Rufai ta aiwatar a Kaduna, Zaria, da Kafancan a ranakun Alhamis da Juma’a.