By Abbas Yakubu Yaura
Al’ummar yankin Basorun da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Juma’a, sun firgita bayan da wata tankar mai ta kama da wuta a wani gidan mai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, tankar tana zuba mai zuwa tankin karkashin kasa da ke Olarem Filling Station a lokacin da gobarar ta tashi a karkashin motar, kuma kafin tankar ta kama da wuta, an ce direban ya tsallake rijiya da baya ya wuce da ita zuwa bakin titi.
Wani mai daukar hoto, Dotun Omiyale, wanda ke zaune a unguwar ya bayyana ta shafinsa na Twitter cewa, an dauki motocin kashe gobara uku zuwa wajen kashe gobarar.