Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnatinsa ta riƙa ciyo bashi daga ƙasashen ƙetare matuƙar ana son a magance matsalar da ƙasar nan ke fama da shi.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kwamitin bayar da shawara kan tattalin arziƙi a birnin tarayya Abuja jiya Talata.
Har wa yau, Muhammadu Buhari ya ce, ciyo bashin kuɗaɗen zai taimaka wajen samar da tituna a ƙasar nan da samar da layukan dogo wanda za su taimaka wajen ceto da rayuwar al’ummar ƙasar nan daga faɗawa cikin mawuyacin hali.
Shugaba Buhari yace babu abinda al’ummar ƙasar nan a yanzu ke fatan samu sama da ayyukan raya ƙasa da zai ƙara bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.