Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a ranar Laraba, ya duba sabon jirgin kasa Talgo mai gudun kilomita 330, a wani yunkurin kammala aikin layin dogo na Red Line dake Legas.
Gwamnan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce, “Titin Layin dokon mai tsawon kilomita 37 da aka kammala zai ratsa tasha takwas tare da kwashe fasinjoji daga Agbado zuwa Oyingbo.”