Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi’u Musa Kwankwaso, ya isa garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a jiya Asabar.
Dubban magoya bayansa ne suka tarbi tsohon gwamnan jihar Kano.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwankwaso, wanda jam’iyyarsa ke shirin rasa daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar Sanata Ibrahim Shekarau, ya ja hankalin jama’a da su zabi NNPP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kananan Hukumomi 47 Na Fuskantar Barazanar Hare-Haren Yan bindiga A Shiyyar Arewa Maso Yamma
A halin yanzu dai Shekarau yana kan hanyarsa ta zuwa jam’iyyar PDP ne sakamakon rigimar da suka yi da Kwankwaso watanni bayan ficewa daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.