Biyo bayan janye dokar kulle da kwamitin kar ta kwana kan annobar sarke numfashi tayi, shugaba Buhari ya gabatar da sallar Juma’a a karon farko bayan dauke dokar a masallacin fadar gwamnatin tarayya.

Wannan shi ne karon farko da aka gabatar da sallah a masallacin tun da aka kafa dokar kulle a watan Mayu.

https://dimokuradiyya.com.ng/shugaba-buhari-ya-karbi-maganin-korona-na-kasar-madagascar/
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yu sallar ne tare da wasu mukarrabansa a yau Juma’a.

Duk da gabatar da sallar Juma’ar Buhari da mukarrabansa sun bi dokar bada tazara tare da amfani da takunkumin fuska, domin dakile cutar Corona.
