Hukumar karɓar koke-koke da yaƙi da cin hanci ta Kano ta musanta zargin da ake yi na cewa hukumar na binciken mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.
Ta hannun shugabanta, hukumar ta fitar da takardar musanta zargin da ake yaɗawa a kafofin sada zumunta cewa mataimakin gwamnan na da hannu a ɓatan wasu kuɗaɗe.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado yace “binciken da muke yi bashi da alaƙa da mataimakin gwamna, Darakta da sakataren ma’aikatar kaɗai ake bincike kuma su ma suna bada haɗin kai yadda ya kamata”.
https://dimokuradiyya.com.ng/ana-binciken-mataimakin-gwamnan-kano-akan-badaƙalar-kuɗaɗen-manoma/
Ya zuwa yanzu hukumar ta samu nasarar dawo da kuɗaɗe sama da Miliyan bakwai.
Rimin Gado ya ƙara jan hankalin jama’a da yi watsi da labarin saboda bashi tushe.