Daga Khadija Mohammed
Wani ma’aikacin lafiya mai suna Dakta Imafidon Osama Agbonile, Ya bayyana cewa likitocin kasar nan wajen dubu talatin da biyar duk sun koma kasar Amurka da sauran kasashen ketare da yin aiki.
Yace a dalilin hakan likitoci sun yi karanci a kasar nan saboda a cikin mutane Dubu biyar yanzu likita daya ne ke duba su Ammadadin mutane dari 600 da ya kamata likita daya ya duba. Wanda hukumar lafiya ta duniya ta zartar wato world health organization(WHO) a Turance.