Wata Kotu a Kasar Pakistan ta yanke hukuncin kisa wa wasu mutane biyu kan laifin da ya shafi bainar jama’a.
Mutanen guda biyu masu suna Abid Malhi da Shafqat Ali Bagga sun tarar da wata yar kasar Faransa mazauniyar Pakistan a bakin titi tare da yayan ta mai ya kare musu.
Wadannan mutane biyu nan take suka kutsa kai cikin motar tata suka mata fyade a idon yayn nata a kan hanyar dake kusa da birnin Lahore.
To sai dai yan sanda sun dora laifi aukuwar hakan ga matar kan cewa ina dalilin ta na fitar ta gaba gadi a kurarren lokaci, to sai dai wannan kalamai ya harzuka yan kasar fita zanga-zanga.
A jiya asabar ne dai kotun ta birnin Lahore tab gurfana da Abid Malhi da Shafqat bisa laifin taron dangi su yi fyade da laifin garkuwa da muatne da kuma fashi da makami.
To sai dai lauyoyin mutanen biyu sun ce ba za ta sabu wai bindiga a ruwa don haka dole su dauaka kara bisa wannan hukunci.