Masu fyade guda 40 ne dubunsu ta cika a Jihar Katsina a watanni biyu da suka gabata, a yayin da matsalar ta fyade da dangoginta ke kara yawaita a faɗin tarayyar Najeriya.
Ana zargin mutum 40 din sun yi wa mata da kananan yara fyade a wasu lokuta da suka saba wa hankali a sassan jihar tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni na shekarar nan.
Yayin sanar da hakan, Kamishinan ‘Yan Sandan Jihar Katsina Sanusi Buba ya bukaci jama’a da su taimaka wurin samar da muhimman bayanai da za su kai ga kama masu mummunar dabi’ar fyaɗe domin kawo karshen matsalar.
https://dimokuradiyya.com.ng/laifukan-fyade-42-aka-tura-kotu-hukumar-yan-sandan-jihar-kano/
Sai dai ya ce ana samun gagarumar nasara a yaki da rundunar ke yi da laifukan fyade a jihar.
Idan ba a manta ba a baya-bayan ne aka dinga samun karuwar rahotannin fyaɗe a fadin Najeriya baki ɗaya, wanda hakan ya jawo kungiyoyi masu zamansu kansu shiga zanga-zanga don ganin gwamnati ta kawo karshen wannan mummunar dabi’a ta fyaɗe.