By Abbas Yakubu Yaura
Sarkin garin Mutumbiyu,kuma Mai shari’a Sani Suleiman (mai ritay), ya yi gargadin cewa daga yanzu makiyayan dake lalata amfanin gona za su biya ainihin kudin amfanin gonakin da aka lalata.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An dauki wannan matakin ne a yayin wani taro da wakilan Fulani makiyaya dana manoma suka gudanar a fadarsa.Mai shari’a Sani Suleiman yace taron ya biyo bayan korafe-korafen da manoman suka yi kan Fulani makiyaya waje lalata musu amfanin gonakin su da suke nomawa.
Ya ce an kafa kwamitocin ne wadanda zasu sanya ido a kan ayyukan da makiyayan ke yi a gundumomin shida domin dakile rikici tsakanin manoma da makiyaya.
Sarkin ya yi gargadin cewa kada makiyaya su kai garkensu zuwa gonaki don lalata amfanin gona da gangan, kuma duk wanda aka samu ya sabawa wannan doka zai biya ainihin darajar amfanin gonakin da aka lalata.
Sannan ya kuma shawarci manoma da kada su yi noma akan hanyoyin shanu da kuma gefen titi wanda ke kawo cikas ga zirga-zirgar shanu.
Ya kuma bukaci mambobin kwamitin da suka hada da manoma da makiyaya da sarakunan gargajiya dasu kasance masu gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukansu wanda ya shafi samar da dawwamammen zaman lafiya a masarautar.
A yayin taron, Yakubu Makurna, wanda ya yi magana a madadin manoman, ya ba da misali da yadda makiyayan suka far wa manoman da suka yi yunkurin korar shanu daga gonakinsu.
“Manoma sun sha wahala sosai a hannun makiyaya saboda barnata amfanin gonakinsu da jikkata da kuma kashe-kashe ta hanyar kai wa manoman da ba su ji ba ba su gani ba hari, wadanda suka yi yunkurin hana makiyaya lalata amfani ln gonakinsu,” inji shi.
Hakazalika, Wakilin makiyayan, Hardo Musa, ya yi ikirarin cewa makiyayan suna nan kan karyewa domin a mafi yawan lokuta manoman suna dora tarar fiye da kimar amfanin gonakin da aka lalata.
Ya bayyana cewa kwamitocin da aka kafa a masarautar kamar yadda Sarkin Mutumbiyu ya kaddamar za su magance rikicin da ke tsakanin kungiyoyin biyu sannan kuma duk Fulani makiyaya suna goyon bayan shirin.
Kazalika a nasu bangaren, Fulanin sun samar da matakan da za su magance matsalar barnatar da amfanin gona da makiyaya ke nomawa a masarautar.