Gwamnan jihar Borno Farfesa Umara Zullum ya ce gwamnonin jihohin yankin arewa maso gabashin kasar nan sun kammala shiryawa domin samar da jirgin sama na yan kasuwa ga yankin nasu.
Gwamna Zulum wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin kasarnan, ya bayyana hakan a yayin zamansu, karo na bakwai wanda ya gudana a Juma’ar nan.
KARANTA ANAN: Dalilin Da Yasa Muke Kashe Makudan Kudade Wajen Gudanar Da Zabe – INEC
A cewarsa wannan kuduri zai taimakawa yankin wanda ya gamu da koma baya ta fuskar kasuwanci shekaru da dama da suka gabata, sakamakon ayyukan yan ta’adda wanda ya kassara yankin nasu.
Ya kuma koka kan yadda yankin nasu gwamnatin tarayya tayi watsi da yankin nasu, musamman waje samar musu da hanyoyin sufuri da mutane da zasu dinga amfani das u domin kasuwanci cikin kwanciyar hankali.
Da yake Magana a yayin taron gwamnan jihar Gombe Muhammad Yahaya yace makasudin taron suna yinsa ne domin duba kan matsalolin yankin, wanda yana daga cikin dalilin da ya sanya suka samar da kungiyar.
A wani labarin kuma: Mutane 15 Ne Suka Rasa Ransu A Wani Jatsarin Mota
Mutane 15 ne suka mutu a daren ranar Alhamis din nan a wani hatsarin karamar motar bas a tsakiyar kasar Guinea, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.
Laftanar Kanar Idrissa Camara, Laftanar Kanal Idrissa Camara, Laftanar da ke kusa da birnin Kouroussa, ya ce “Wata karamar motar bas cike da fasinjoji tare da gawa a Bissikirima, kusa da Dabola (a tsakiyar Guinea), ta kife, inda tayi sanadiyyar mutuwar mutane 14 a nan take.”