Wakilinmu Muhammad Gambo Damaturu
Wasu matasa guda uku sun Samar da wata sabuwar hanyar Hudar gona a Damaturu, sakamakon rashin kudin hayan garma da karancin kayan noman zamani, da suke Fuskanta a Jihar Yobe.
Da suke bayani ga Wakilin Jaridar Dimokuradiya: a birnin Damaturu, Matasan, Musa Muhammad, Musa Ali da Muhammad Musa, wanda shekarun su bai wuce 20, 18 da 19 ba kamar yadda suke a jere, sukace sun nemi Hayan garman shanu domin yin Hudar gonar su amma basu samu ba sakamakon tsada da kuma karancin sa.
Hakan ne yasa sukayi tunanin karban aron garmar makwabcin su don Hude gonar su.
Matasan, sun bayyana cewa ba kowa bane zai iya hayan garman shanu ko Tarakta ba saboda tsada da kuma karancin kayan a Yankin.
Sun kara da cewa yanzu haka sun fude gonar su mai fadin safiya daya a cikin yini biyu.