Hukumar gudanarwar jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife ta Kori wani Malami dake koyarwar a sashin horas da harshen Turanci, bisa kamashi dumi-dubu da zargin yin lalata da wata dalibar makarantar.
Bayanin haka na kunshene a cikin wata sanarwa da jami’in Hulda da jama’a na Jami’ar Abiodun Olarewaju ya fitar, wacce Kuma yasanya wa lakabi da “Yin lalata da Dalibai: Jami’ar OAU ta kara sallamar Malami” a yau Talata.
Inda sanarwar ta yi nuni da cewa, “A yunkurin jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife, na dakile cin zarafin Dalibai ta kowace fuska, hukumar Gudanarwa ta jami’ar ta sake Koran wani Malami bisa kamashi Dumu-Dumu da aka yi, da yin lalata da wata dalibar makarantar.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Taliban: Ba zamu haramta Kafafen sada zumunta na zamani ba
Kazalika sanar war ta ce, ” An yanke shawara Koran Dakta Adebayo Mosobolaje na Sashin horas da harshen Turanci ne a yau Talata 7 ga watan Satumban shekarar 2021.” Inji sanarwar.
“Kuma jami’ar ta dauki wannan matakin ne, bisa dubi akan rahoton da kwamitin hadin gwaiwa da majalissar Dattijan jami’ar suka gabatar, Wanda ya nuna cewa, tabbas Mosobolaje ya aikata laifin da ake zarginsa da shi, Wanda hakan yasa dole ya fuskanci hukuncin dokar gudarwa na jami’ar”.
Sai dai Koda majiyar jaridar Dimokuradiyya ta tuntumi Mosobolaje domin ji ta bakin shi, bai dauki waya ba, kazakika bai amsa sakon kartakkwana ba.