Gwamna Simon Lalong na jiharb Filato a ranar Alhamis ya taya Malam Yakubu Mohammed bisa sake sabunta masa wa’adinsa a matsayin babban Daraktan Talabijin na kasa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa; shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake sabunta wa’adin Mohammed ne har na tsawon shekara uku a matsayin shugaban NTA din bayan wa’adinsa ya kare cikin watan Mayu.
Lalong, bayan taya shugaban NTA din dan asalin jihar Filato a yayin da ya kai masa ziyara a Jos, inda ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Buhari bisa zabarsa aka sake damka masa wannan mukamin. Ya mika godiyarsa ga shugaban NTA din bisa yadda aka yada shi sosai a wa’adin mulkinsa na farko, ya kuma roki a nunka hakan a wa’adin mulkinsa na biyu.
Lalong ya nemi Daraktan NTA din da ya bai wa ‘yan asalin jihar Filato musamman matasa guraben aiki.