Shahararriyar yar wasan Tennis ɗin nan Ashley Barty ta bugi kirjin cewa ta chanchanci matakin lamba ɗaya a fagen Tennis ɗin duniya bayan da ta chasa Bianca Andreescu a gasar Miami Open ranar Asabar.
Yar wasan mai shekara 24 yar asalin ƙasar Austaraliya ta matsa kaimi matuka a wannan kaka inda ala tilas sai da wanke Andreescu ci 6-3 da 4-0 a gasar.
Da ma dai tun da farko Barty ta bayyana chanchantarta ta zama lamba ɗaya a duniya, ko da yake kalaman nata ya gamu da suka da dama daga abokan karawarta na Tennis a duniya, to amma nasararta ta ranar Asabar ɗin ka iya rufe bakin su.