Nyesom Wike gwamnan Jahar Rivers ya misanta Laurette Onochie a matsayin Shugabar hukumar INEC, yana mai zargin jam’iyyar APC da shirin murde zaben 2023 mai zuwa.
Ya bayyana hakane a Port Harcourt, wajan bikin cikarsa shekara shida da mulki, inda yake nuna cewa zaban Laurette da Shugaba Muhammadu Buhari yake nufin yi cibaya ne ka siyasar kasa. Kamar yadda Jaridar Channel Tv ta wallafa a shafinta
“Duk da cece-kucen kan nadata a matsayin Shugabar hukumar INEC duba da rashin cancantar ta da kuma rashin adalcin ta, shugaban Yan majalisun Dan APC na kokarin tabbatar da ita don nufin murde zabe mai zuwa, duk da cewar sun san Yan Najeriya ba za su zabesu ba idan za’a gudanar da zabe na adalci.
KARANTA:- Sabbin jami’ai: Rundunar sojin ruwa ta karyata labarin sunaye na Musamman, ta yi gargadi
Ya nuna Laurette Onochie a matsayin yar gani kashenin APC, ya kuma nuna zabenta ta Buhari yayi ba akan gaskiya bane.
Yayi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya janye akan nadata a matsayin Shugabar hukumar INEC.
“A matsayi na na gwamna kuma mai kishin Yan Najeriya kuma mai son cigaban siyasan kasar nan, dole na shawarci shugaba Muhammadu Buhari daya janye akan nada Laurette Onochie don gujewa matsaloli da ka iya faruwa da hukumar INEC da kuma lokacin gudanar da zabe.”
Wike ya kiraga Yan majalisu da su tashi tsaye wajan kare kasa.
Wike ya tunama mutane da cewar shugaba Buhari yayi nasarar cin zaben sa na 2015 da 2019 don alfarmar Card Reader da tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kawo a lokacin Mulkin PDP.
Yayi mamakin kan irin yadda Shugaban Kasa ke nuna ko in kula wajan tabbatar da tsaftataccen zabe.
Bayanin Wike ya biyo bayan kwaniku hudu da Yan majalisu suka fara tantance Laurette Onochie a matsayin Shugabar hukumar INEC.
Misis Laurette Onochie mataimakiyar shugaban Kasa ta fannin kafafen sada zumunta, wanda ya zabeta a shekarar da ta wuce a watan Octoba.
Kwamitin suna cigaba da tantace mutane hudu da wadanda shugaba Buhari ya zaba don zama shugaban hukumar INEC., Wadanda suka hada da Kunle Cornelius, Saidu Ahmad, Sani Adam da kuma Baba Bila.
Comments 1