Daga: Abbas Yakubu Yaura
Inibehe Effiong, lauya mai fafutukar kare hakkin bil’adama, ya sake samun ‘yancinsa bayan ya shafe wata guda a gidan yari a Uyo, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
An ga Mista Effiong a cikin wani faifan bidiyo kai tsaye yana fita daga gidan yari ga hannun abokan aikinsa wadanda suka taru a kusa da Wellington Bassey Way, Uyo, da karfe 8:00 na safe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojojin Najeriya sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari
Mai shari’a Ekaette Obot, a ranar 27 ga watan Yuli, ta daure Mista Effiong a gidan yari bisa zargin cin mutuncin kotu bayan da aka ruwaito lauyan ya nuna rashin amincewa da kasancewar ‘yan sanda dauke da makamai a gaban kotu.
Lauyan mai kare hakkin dan Adam ya kasance a kotun ne domin kare Leo Ekpenyong, lauya, a karar da Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom ya shigar.
A shari’ar da ta gabata, Mista Effiong, lauyan da ke Legas, ya bukaci Ms Obot da ta janye kanta daga shari’ar.
A wani labarin kuma PTA ta Ƙaryata batun bayar da dubu Goma-Goma don kawo karshen yajin aikin ASUU
Kungiyar iyayen yara ta Najeriya ta karyata maganar cewa za ta bayar da gudunmawar Naira 10,000 kowannensu ga daliban Najeriya, ga kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, domin kawo karshen yajin aikin na watanni 6.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Alhaji Haruna Danjuma ya fitar, ya nesanta kungiyar daga wannan ikirarin.