Kungiyar lauyoyin Najeriya wato NBA ta umarci ‘ya‘yanta da su kauracewa Kotuna a fadin kasar nan har na tsawon kwana biyu, wanda zai fara daga Yau Talata, da kuma Gobe Laraba, domin nuna rashin amincewarta da dakatar da alkalin alkalai na kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi ba tare da bin ka’idar doka ba.
Kungiyar ta cimma wannan mataki ne a zaman gaggawa da ta kira a Jiya Litinin a Abuja, ga masu ruwa da tsaki kawai na kugiyar.
Ta Umarci duk wani Lauya cikakken dan kungiyar, a fadin kasar nan da kar su shiga Kotunansu har na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da zaga-zagar rashin goyon bayan dakatarwa da aka yi wa Alkalin Alkalan na kasa.
Hakan na nufin maimakon lauyoyi su kasance a Kotunansu domin rage yawan shari’a da ke gabansu za su bazama yin zanga zanga har na tsawon kwana biyu.