Ministan Sufuri na tarayyar Najeriya, Mu’azu Sambo, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta mayar da hankali wajen ganin an kammala aikin layin dogo na Kano zuwa Kaduna a kan lokaci.
Da yake jawabi a lokacin da yake duba aikin jirgin kasa a garin Yako da ke karamar hukumar Madobi a Kano, Sambo ya ce aikin wani muhimmin abu ne da zai kara wa kasar nan daraja.
“Muna iya bakin kokarinmu don ganin aikin ya samu nasarar kammaluwa akan lokaci.
DUBA WANNAN LABARIN: FG ta gina cibiyar samar da injinan noma a Nassarawa
“Ana noma amfanin gona a Arewa kuma ana kai su Kudu yayin da kayayyakin da ake shigo da su kasar nan suna zuwa daga tashar ruwa,” in ji shi.
Sambo ya ci gaba da bayanin cewa manyan kalubale biyu da aikin yake fuskanta sune kare lafiyar ma’aikata da kuma mamaye filayen da aikin ya rutsa ta cikin su.
Dangane da batun kare lafiyar ma’aikata, ya ce ma’aikatar za ta tabbatar da tsaron da ya kamata, don kawar da barazanar tsaro a wuraren dake akwai.
Hakazalika, Babban Darakta na Kamfanin da ke gudanar da wannan aiki, Filippo Macchioni, ya danganta tafiyar hawainiyar aikinsu da daidaitawa daga layi daya a baya, zuwa layuka biyu a yanzu.
“Mun yi yarjejeniya da ma’aikatar ayyuka kan kammala aikin nan da watanni 36 a baya, yayin da yanzu kuma an sauya shi zuwa watanni 18.”