By Abbas Yakubu Yaura
Wasu maniyyata aikin hajji a jihar Legas a ranar Litinin sun mamaye gidan gwamnatin Alausa domin nuna rashin amincewarsu da karin kashi 100 cikin 100 na farashin kudin Hajjin shekarar bana 2022.
Alhazan sun ce tuni sun biya kudin aikin Hajjin shekarar 2020 tun daga shekarar 2019 da ba a yi ba saboda annobar COVID-19.
Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Ya Kashe Gomman Mutane Tare Da Lalata Dukiya A Kasar Rwanda
Sun ce abin ya ba su mamaki, sun samu sako daga Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar cewa zasu biya karin Naira miliyan 1.3 domin daidaita kudaden da aka biya tun a shekarar 2019.
Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce su wakilan maniyyata ne daga dukkan kananan hukumomin jihar, ya ce, “Mun zo ne domin neman biyan bashi.
Ya kara da cewa Makonni uku da suka wuce, Kwamishinan ya gayyace mu zuwa tsohon shingen sakatariya. Sai aka ce mana za su kara kudi ne kawai amma sai muka ce kada su yi yawa idan an kara.
“Mun biya Naira miliyan 1.3 a shekarar 2019, abin mamaki, a ranar Juma’a, mun samu sakon karin Naira miliyan daya da dari uku da arba’in 1,340,000, wanda ya kai naira miliyan biyu da dubu dari shida da arba’in 2,640,000, fiye da kashi 100. Kuma yanzu suna ba mu wa’adin kwanaki biyar na aikin hajjin shekarar 2019, 2020-2021 da kuma 2022.
Sun bukaci gwamnan jihar, Mista Babajide Sanwo-Olu da kakakin majalisar, Mudashiru Obasa su shiga tsakani kan lamarin.
“Mun roki Gwamnanmu da Shugaban Majalisar jihar Legas kuma muna neman zaman lafiya,” inji shi.