By Ishaq Dabai
Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya NNS BEECROFT, dake Apapa, ta jihar Legas, ta ce a ranar litinin ta cafke mutane 16 da ake zargi da fasa bututun mai a ban garen Abagbo na bututun mai na NNPC.
Kwamandan rundunar sojin ruwa NNS BEECROFT, Bashir Mohammed, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa,inda ya ce an kama mutanen ne ranar Juma’a bayan da rundunar sojojin da ke Atlas Cove suka sami rahiton bayannan sirri na masu aikata laifin.
Ya ce, an cafke wadanda ake zargin da fasa bututun man da keguna 73 mai daukar lita 50,da kekuna 18 mai daukar lita 25, kowanne cike da kayayyakin da ake zargin Premium Motor Spirit PMS ne da fiber guda biyu da ke da 175 HP kowannensu.
Baya da haka an kama wasu yayin gudanar da wani sintiri na tashar jiragen ruwa na yau da kullun a rafin da ke kusa da tsibirin maciji, ”in ji shi.
A cewarsa, kamen zai aika da sako izuwa masu aikata laifuka na fasa butun mai na kudurin Sojojin ruwan Najeriya bisa rashin jin dadinsu ga barna ta fasa bututun mai.
Mohammed ya ce an mika wadanda ake zargin zuwa ga hukumar Tsaro ta Najeriya NSCDCdon gurfanar da su a gaban kotu.
Kazalika ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin kudirin rundunar sojojin ruwa na ci gaba da ayyukanta bisa kundin tsarin mulki wanda ya hada da dakile haramtattun ayyuka a cikin gabar ruwan Najeriya.