By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili a jihar inda ya zama doka.
Sanwo-Olu ya amince da kudirin a gidan gwamnatin jihar Legas ranar Litinin, wannan na zuwa ne kwanaki 11 bayan majalisar dokokin jihar ta zartar da dokar da ta haramta kiwo a fili a jihar.
Bayan zartar da kudirin a ranar 9 ga watan Satumba, Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa ya yabawa takwarorinsa bisa shakuwar da suke yi na ganin jihar ta ci gaba da bunkasa.
Batun kiwo a fili ya kasance mai daukar hankali a kasar domin ya haifar da sabani tsakanin gwamnonin kudu da makiyaya.
A wani mataki na dakile kashe kashen, gwamnonin kudancin sun yi taro a Legas a ranar 5 ga watan Yuli kuma sun cimma matsaya mai yawa kan kiwo a fili, sake fasalin Najeriya, tare da yin kira ga ‘yan sandan jihohi.Bayan taron, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudancin, Rotimi Akeredolu, ya ce gwamnonin sun amince da wa’adin da aka bayar na fitar da dokar hana kiwo a tsakanin mambobinta.
Comments 1