By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Legas, Mista Bababjide Sanwo-Olu, ya bayyana aniyarsa ta hukunta masu laifi dake da hannu a hare haren da ake kaiwa jami’an tsaro a jihar, inda ya sha alwashin za a gurfanar da su a gaban kuliya.
A wani ci gaban kuma, Sanwo-Olu, ya bada tabbacin jajircewar gwamnatinsa na kara samar da isasshen sarari ga matasa don bunƙasa kasuwanci da shugabanci a zaman wani ɓangare na matakan ƙarfafa musu gwiwa a aikin gina ƙasa na Najeriya.
Gwamnan, wanda ya lura da tsananin damuwa kan yawaitar kai hare hare kan jami’an tsaro, ya bayyana irin wadannan hare hare “marasa ma’ana” a matsayin kokarin tattake doka da oda daga wadanda ke matukar son juyar da al’umma baya, “ba za a yarda da hakan ba. A cikin sabbin hare haren, an kashe babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, CSP, Kazeem Abonde a ranar 23 ga Satumba, 2021, a Ajao Estate da wasu ‘yan daba da ba a san su waye ba.
A cewar Sanwo-Olu, “Na umarci Kwamishinan‘ yan sanda daya tabbatar an gurfanar da duk wadanda suke da hannu cikin wannan mugun aikin.
“Ba za a yarda da irin wannan nuna halin dabbanci kamar yadda CSP Abonde ya mutu a cikin jihar mu ba, komai yanayin.
“Dokar tana nan a gare mu duka idan akwai bukatar a gyara duk wani laifi da aka gani.Jama’ar dake ɗaukar doka a hannunsu masu tallata shari’ar daji ne, wanda ba za a bari ya sami gindin zama a cikin jihar Legas ba.
Gwamnan, yayi wannan jawabin ne a jiya a wani haɗin gwiwar Matasa na Legas na kwana ɗaya, tare da taken: ‘Matasa da ɗabi’a a cikin Al’umma mai tasowa: Kalubale da Shawarwari’, wanda Ofishin Uwargidan Shugaban Ƙasa ta shirya, wanda keda mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat daya halarta, ya bukaci matasa da su yi amfani da lokacin su yadda ya dace domin hakan zai kara musu kima a nan gaba da ci gaban al’umma.