By Ishaq Dabai
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da mataimakin shugaban sojin sama Smith mai ritaya a Legas.An yi garkuwa da AVM Smith (mai ritaya) da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin a wurin da ke kusa da Blenco Mall dake kan titin Addo Ajah a Legas.
An samu labarin cewa ‘yan bindigar da suka yi harbi ba kakkautawa cikin iska sun sace AVM Smith yayin da direbansa ke gudanar da aiyuka.
A cewar wani wanda abin ya faru a kan idonsa, harbin bindiga akan iska yayin da ‘yan bindigar ke harbe harbe wanda hakan ya tilastawa mutane tserewa don tsira da rayuwar su, yayin da babbar kasuwar Blenco ta rufe kofar shiga cikin ta.
Rahotonni sun bayyana cewa yan bindigan bayan sunyi garkuwa da AVM sun tsere a cikin kwalekwale mai sauri ta cikin ruwa.
A cikin sakon muryar da direbansa ya aiko, kofur Okdiji wanda ke da alaƙa da AVM Smith mai ritaya, an ji yana cewa, “sun sace Smith daga wurin da muke. Wasu ‘yan bindiga sanye da abin rufe fuska sun sace shi.
Suna harbi ko’ina, ina gyaran motar oga, lokacin da abin ya faru. A kan hanyata ta dawowa na gan su.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas CSP Adekunle Ajisebutu yace zai mai da martani daga baya.