Shekaru 2 bayan nadin Brendan Rodgers a matsayin mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, da alamun ya iya rusa tarihin Firimiya wajen kai tawagar ga nasarar karkare kakar bana a jerin ‘yan shidan saman teburi baya ga bata damar zuwa gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko.
Leicester, yanzu haka na matsayin na uku ne teburin Firimiya sama da Liverpool mai rike da kambun da tazarar maki 3, dai dai lokacin da kungiyoyin biyu ke shirin haduwa a yau asabar, haduwar da ke matsayin cikakkiyar dama ga Leicester na kara yawan tazarar da ke tsakaninta da Liverpool, dai dai lokacin da tawagar ta Jurgen Klopp ke ci gaba da barin maki a kusan kowanne wasa.
Cikin wasanni 11 da Liverpool ta doka a baya-bayan nan 3 kadai ta iya nasara yayinda ta gamu da mummunan kaye har gida a hannun Manchester City makon da ya gabata da kwallaye 4 da 1.
Matukar Leicester ba ta maimata kuskuren da ta yi a bara ba, ko shakka babu za ta iya karkare kakar a matsayin ta 3 ko ta biyu a teburin Firimiya.
Sai dai ko a bara tawagar ta Brendan Rodgers da ke matsayin tsohon kocin Liverpool ta yi barin maki ne a watan karshe na karkare wasannin gasar ta yadda ta gaza karkarewa a jerin ‘yan hudu.