By Abbas Yakubu Yaura
Yin rijistar Seif al-Islam Kadhafi, dan marigayi Moamer Kadhafi, don tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a yi a wata mai zuwa ya haifar da cece-kuce a tsakanin ‘yan kasar Libya.
Zaben shugaban kasa na farko a Libya kai tsaye da za a yi a ranar 24 ga watan Disamba, zai zama kololuwar tsarin da Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar a shekarar data gabata, na kokarin yin layi tsakanin shekaru da dama da aka shafe ana tashe tashen hankula tun bayan boren da ya kifar da gwamnatin Kadhafi a shekara ta 2011.
“Ina kallon nadin Seif a matsayin rashin adalci, domin har yanzu kotun hukunta manyan laifuka ta duniya tana neman sa, kuma yana da hukunce-hukunce da yawa a kansa, baya ga cewa shi mutum ne mai yawan cece-kuce.” a cewar Nizar al-Hadi, mazaunin Tripoli.
(Idan mutanen Libya suka yarda da Seif) to zamu manta da abin da ya gabata. Idan aka yi afuwa na gama-gari kuma aka kula da wasu muhimman batutuwa kamar kudin jama’a da laifukan yaki, ba tare da akwai batutuwan cikin gida da daukar fansa ba, to ina ganin zai iya yin nasara kuma Libya za ta bunkasa.”
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) wanda take neman sa ruwa a jallo bisa laifukan cin zarafin bil adama da ake zargin an aikata a lokacin boren da kungiyar tsaro ta NATO ke marawa baya, Seif al-Islam ya kammala “dukkan sharuddan doka da ake bukata”, in ji hukumar zaben a ranar Lahadi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Seif al-Islam Kadhafi ya mika takardunsa na neman tsayawa takar na zaben shugaban kasa zuwa ga ofishin hukumar zabe ta kasa dake birnin Sebha, “in ji sanarwar.
Hukumar ta fitar da hotuna da ke nuna Seif al-Islam sanye da rigar gargajiya.An ba shi katin zabe na gundumar Sebha ta kudu.
A ranar Litinin din data gabata ne kasar Libiya ta bude yin rajistar ‘yan takara a rumfunan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.