Lionel Messi ya ci kwallonsa ta farko a gasar Ligue 1 ranar Asabar a lokacin da Paris Saint-Germain ta samu jan kati da aka bai wa mai tsaron gida Keylor Navas inda ta doke Nantes da ci 3-1.
Kylian Mbappe ya ci gaba da zura kwallo a raga a filin wasa na Parc des Princes, amma Randal Kolo Muani ya rama wa Nantes a bayan da aka bai wa Navas jan kati.
Kwallon da Dennis Appiah ya zura ne ya sa PSG ta dawo gaba ana saura minti 10 kafin Messi ya kammala baiwa PSG nasara ta 12 a wasanni 14 a kakar wasa ta bana, gabanin wasan da kungiyar za ta yi da Manchester City a gasar zakarun Turai mako mai zuwa.
Tawagar Mauricio Pochettino ta kara bada tazara tsakanin ta da kungiyar Lens da maki 13.