By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Larabar da ta gabata ne likitocin asibitin koyarwa na jami’ar Ondo suka fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu domin nuna rashin amin cewarsu da harin da dan uwan wani majiyyaci ya kai wa daya daga cikinsu.
An tattaro cewa wani likitan da ke asibitin, mai suna Dakta Sayo, an yi zargin dan uwan wani majiyyaci ne ya kai masa hari.
Sayo, wani jami’in kiwon lafiya da ke aiki da sashin bada agajin gaggawa na asibitin an kai masa hari ne a lokacin da yake gudanar da aikinsa.
An tattaro cewa dan uwan majinyacin ya afkawa likitan wanda ya zarge shi da rashin kula da tsofaffin majinyata dake asibitin yadda ya kamata.
A saboda haka ne likitocin a karkashin inuwar kungiyar likitoci ta UNIMEDTH suka gudanar da zanga-zangar lumana a rassan asibitocin Ondo da Akure a lokaci guda, inda suka bayyana harin a matsayin na dabbanci.
Sun yi kira ga gwamnatin jihar data samar da isasshen tsaro a asibitin don hana sake afkuwar irin wannan lamari anan gaba.
Da yake jawabi yayin zanga-zangar, shugaban kungiyar, John Matthew, ya ce harin da aka kai wa abokin aikinsa ba shi da wata bukata.
Sannan ya ce, “Abin takaici ne yadda muka tsinci kanmu a cikin wannan mawuyacin hali. Sama da ma’aikata 100 ne suka bar asibitin, wanda hakan ya kawo mana nauyi.
“Muna rokon gwamnatin jihar da ta dauki karin likitoci domin magance matsalar. Muna kuma son gwamnati ta samar da isasshen tsaro a asibitin.”
A halin da ake ciki, mahukuntan asibitin sun yi tir da harin da aka kai wa likitan.
Babban Daraktan Asibitin, Dokta Oluwole Ige, ya bayyana haka a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai kan lamarin.
Ige ya kuma yi Allah-wadai da matakin da likitocin masu neman kwarewa suka dauka na shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu kan harin da aka kai wa abokin aikinsu, yana mai cewa yajin aikin bai dace ba tunda an kama mai laifin.
Kazalika ya ce, “Ba daidai ba ne dan uwan kowane majiyyaci ya kai wa wani ma’aikacin lafiya hari. Ba kawai dabbanci ba ne, amma rashin hankali.Jami’an Amotekun sun kama mutumin da ya ci zarafin likitan, kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya daga yanzu.
“Amma hukumar gudanarwar ba ta ji dadin matakin da likitocin suka dauka na shiga yajin aikin gargadi ba.Shawarar su ba daidai ba ce kuma ba ta da kyau ga tsarin kiwon lafiya.Hukumar ba ta ji dadin ci gaban da aka samu ba.”