Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa ta yi barazanar sake shiga yajin-aiki daga ranar Litinin, 7 ga watan Satumba.
Ƙungiyar a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Dakta Aliyu Sokomba, sakatarenta Dakta Bilqis Mohammad, da sakataren yaɗa labarai, Dakta Egbogu Stanley, ta ce za ta shiga yajin-aikin ne bayan da wa’adin kwana 21 da ta ba gwamnati sun ƙare a ranar 17 ga watan Agusta.
Likitocin dai na buƙatar gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da su, ta kuma biya su kuɗaɗen alawus-alawus na yaƙi da annobar Korona da kuma basukan albashin da suke bin ta na shekarun 2014, 2015 da 2016.
Idan za a aiya tunawa, a ranar 15 ga watan Yunin da ya gabata ne ƙungiyar ta fara wani yajin-aikin sai baba ta gani kafin daga bisani ta janye shi ranar 22 ga watan bayan da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki suka sa baki.
Ƙungiyar ta ce, “Majalisar zartarwar ƙungiyarmu ta yanke shawarar shiga yajin-aiki daga ƙarfe takwas na safiya ranar Litinin, 7 ga watan Satumbar 2020, har sai an cika waɗannan sharuɗɗa; biyan mu kuɗaɗen horon neman ƙwarewa da muke bi kamar yadda aka amince a kasafin kuɗin 2020 da aka yi wa kwaskwarima; da samar da ingantaccen tsarin inshorar lafiya ga dukkannin ma’aikatan lafiya.
Har wa yau, sai an biya mu bashin kuɗaɗen alawus ɗin aikin annobar Korona da muke bi; sabunta biyan kuɗaɗen alawus da aka amince za a biya mu a tattaunawarmu ta baya da masu ruwa da tsaki; biyan mu giɓin albashin da muke bi na shekarun 2014, 2015 da 2016,” inji ƙungiyar.
Likitocin sun kuma ce dole a biya dukkannin masu aiki a cibiyoyin lafiyar manyan makarantun gwamnatin tarayya da na jihohi hakkokinsu kamar yadda sabon tsarin biyan mafi ƙarancin albashi ya yi tanadi.
Galibi dai ƙungiyoyin ma’aikata kan shiga yajin-aiki domin neman wasu haƙƙoƙinsu a Najeriya, wada hakan ke zama hanya daya tilo da hukumomin ke share musu hawaye.