Kungiyar likitocin cikin gida na kasar nan ta bawa gwamnatin tarayya kwanaki 14 domin cika alkawarin da ta dauka musu ko kuma sun tsunduma yajin-aikin sai baba ta gani.
Kungiyar ta fitar da wannan jawabi ne a karshen wani zaman tattaunawa da ta yi da wakilan ‘ya’yan kungiyar na kasa baki daya a yau Asabar a jihar Bauchi.
Kungiyar ta bayyana halin damuwa da gwamnati ke nunawa na rashin kulawa ga ‘ya’yan kungiyar nasu.
Shugaban kungiyar na kasa Dakta Sokomba Aliyu, ya nuna damuwarsa game da irin cin zarafin da hukumomin tsaro ke nunawa ‘ya’yan kungiyar a irin jihohin Legas, Kaduna, Plateau da kuma babban birnin tarayya a yayin zuwansu wajen aiki.
Ya nuna rashin jin dadinsa na korar ‘ya’yan kungiyar tasu har mutane 26 daga bakin aikinsu daga asibitin koyarwa na Jami’ar Jos dake Plateau, wanda yake ganin an fi bukatarsu a yanzu sama da kowane lokaci duba da yanayin da ake ciki na annobar COVID19.
https://dimokuradiyya.com.ng/duk-da-korona-likitoci-sun-shiga-yajin-aikin-a-legas/
Har wa yau, Aliyu ka soki gwamnatin Kaduna wajen rage kaso 25 na albashin likitocin jihar.
“Muna kira da babbar murya domin a sake duba tare da biyanmu dukkanin alawus dinmu da ya shafi aikinmu, wanda ya hada da alawus na yaki da cutar COVID19”.
“Kungiyarmu ta NARD na kira ga jami’an tsaro da su daina tsangwamarmu da kyararmu a yayin tafiya ayyukanmu. Sannan mun bawa gwamnati kwanaki 14 da a biya mu dukkanin kudadenmu ko kuma mu shiga yajin-aiki”.
Shugaban kungiyar ya sake kira ga gwamnati da ta samar musu kayan aiki na kariyar kai a yayin aiki, kuma dole ne a tabbatar da an kai su ga kowanne asibiti dake fadin kasar nan.