Kungiyar Likitoci na Asibitin gwamnatin tarayya dake Jabi Abuja, sun janye yajin aikin da suka shiga.
Dr Adejo Arome, shugaban kungiyar shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani zaman gaggawa da kungiyar suka kira, inda ya ce shugabannin asibitin sun nuna damuwa tare da ba da gudummawa wajen janye yajin aikin.
Ya jinjinawa hukumomin asibitin bisa tallafin da suka ba su a lokacin yajin aikin, tare da jinjinawa Daraktan asibitin bisa fahimtarsu da suka yi a yayin yajin aikin.