Wata likitar dabbobi da ke TikTok ta bayyana yadda jama’a suka fafutuka suna sadaukar da rayuwarsu sanadiyyar neman abinci, YEN.com.gh ta ruwaito.
Kamar yadda likitan ta nuna, likita na tsaka da aiki kan zakin da suka yi wa allurar bacci, kwatsam sai y falka kafin lokacin da suka sa ran zai kai.
KU KARANTA: Ko sisi ba zan bata ba, ta yi wa zumunci, Ɗan Achaɓa ya murje ido ya ƙi biyan mata kuɗin babur ɗinta
Nan da nan ma’abota amfani da kafar sada zumuntar suka dinga tsokaci kala-kala kan yadda gabadaya masu aiki kan dabbobin dajin suka tsere yayin da suka ga zakin ya fara motsi.
Kowa ya san yadda zaki yake da matukar hatsarin gaske, hakan ke sanyawa idan za a yi aiki akan shi sai an yi masa allura mai karfi wacce za ta sanya shi bacci.
A wannan karon kuwa an samu akasi, kasancewar likitan ya yi zaton allurar zata dade tana aiki akan zakin sai kuma lamarin ya sha bambam.
Nan da nan mutane suka dinga tsokaci kan yadda mutane har 7 da ke aiki kan zakin suka tsere a rikice.
Wani Paul Delaney Delaney ya ce:
“Wasa ne wannan mai sauki, wanda ya tsaya a baya ne zai dandana kudarsa.”
Marvin ya ce:
“Inda kadai za ka iya gani na shi ne a matsayin direba. Yadda da zarar na ga ya falka kuna fara ihu zan ja mota in tsere.”
Meme-Snows world yace:
“Nan da nan duk duka tsere.”
Number77 yace: “
Kowa na ta kuri sai da suka ga ya falka sannan suka ankare.”
Jaystar Kay tace:
“Akwai wanda ya tsere ya bi hanyar da sakin yake.”
Yadda Sule ɗan achaɓa ya cika bujensa da iska bayan budurwar da su ke lalata ta sheƙa lahira
Ana zargin Sule ya kebe da budurwa mai suna Muniat a ranar Juma’a da dare, amma kuma aka neme shi aka rasa bayan an ga gawarta a karamar hukumar Igbogbo Bayeku da ke Jihar Legas, Nigerian Pulse ta ruwaito.
An tattaro bayanai ka yadda mai kula da masaukin bakin ya duba dakuna kamar yadda ya saba inda ya tsinci gawar Muniat.
Bayan ganin hakan ne yasa mai kula da masaukin bakin yayi gaggawar sanar da caji ofis din Ikorodu, bayan nan ne jami’an ‘yan sanda su ka ci gaba da bincike.
A bayanin da yayi, kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya shaida cewa jami’ansu sun je wurin inda su ka tabbatar cewa babu wata alamar azabtarwa a jikin Muniat.