Kungiyar likitocin kasar Italiya sun ce mambobin su sama da 150 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Korona, yayin da da suke aikin ceto rayuwar jama’a.
Kungiyar likitocin tace zuwa ranar 9 ga wannan wata na Afrilu, likitoci 100 suka mutu, amma a halin yanzu adadin ya kai 151.
Shafin Rfi Hausa sun tabbatar da cewa; a jiya kawai mutane 333 suka mutu a Italiya abin da ya kara yawan mutanen da suka mutu sakamakon wannan annoba a kasar zuwa dubu 26 da 977.
Firaminista Giusseppe Conte ya bayyana shirin bude kofofin kasar domin baiwa jama’a damar walwala daga ranar litinin mai zuwa