Likitoci a faɗin Ƙasar Turkiyya sun fara yajin aiki na kwana biyu a ranar Alhamis, inda suke zanga-zanga akan ƙarancin biyan Albashi, da rashin kyakkyawan yanayi, a yayinda da ƙasar ta fara fuskantar mummunan yanayin matsin tattalin arziki, fiye da shekaru 20 da suka gabata.
Mambobin Ƙungiyar Likitoci na cikin Gida Hekim-Sen da suka haɗa da Likitocin iyali da na bada taimakon gaggawa, sun daina aiki, ƙungiyar ta kuma ta bada umarnin a riƙa tura hotonnin babu kowa daga garuruwa da dama na Kafafen Sadarwa na Zamani
- KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani: Majalissun Tarayya Sun Amince da Gina Cibiyar Lafiya A Rigasa
Ƙungiyar ta bayyana ayyuka masu yawa, da cin mutunci daga marasa lafiya a matsayin dalilan yajin aikin.
Kimanin Ma’aikata 316, majinya ta suka kai masu hari a cikin hare-hare 190 a Shekarar 2021 a Ƙasar Turkiyya, a cewar wata Ƙungiya Saglik-Sen.
Da yawa daga cikin magidanta a Ƙasar Turkiyya suna ƙoƙari su magance rashin kuɗi, a yayinda aka samu Hauhawar farashi a shekaru 20, da kuma na Abinci, da kayayyakin more rayuwa.
A ranar Laraba, Shugaban Ƙasa Recep Tayyib Erdogan yace wannan Hauhawar farashin na wani lokaci ne, kuma dole ƴan ƙasa suyi haƙuri na wani lokaci.
Sama da Likitoci 1,400 suka bar Kasar Turkiyya a Shekarar 2021 inji Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasar Turkiyya (TTB).