Wani babban bam da aka jiye ranar Juma’a a daya daga cikin manyan masallatai a yammacin Afghanistan ya kashe akalla mutane 18, ciki har da wani limami mai fada a ji wanda a farkon wannan shekarar ya yi kira da a fille kan wadanda suka aikata “aiki mafi kankantar laifi” kan gwamnati.
Hotunan da aka wallafa a shafin sada zumunta na Twitter sun nuna wasu gawarwaki masu dauke da jini a warwatse a harabar masallacin Gazargah da ke birnin Herat.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna Daga Jam’iyyar
Tashe-tashen hankula sun ragu sosai tun bayan da Taliban ta koma kan karagar mulki a bara, amma wasu bama-bamai da dama da ke auna kananan kabilu – sun girgiza kasar cikin ‘yan watannin nan, da dama daga kungiyar IS mai da’awar jihadi.
Akalla mutane 18 ne suka mutu sannan wasu 23 suka jikkata a harin na ranar Juma’a, in ji Hameedullah Motawakel, kakakin gwamnan lardin Herat, a wani sako da ya aike wa manema labarai.
Kakakin gwamnatin kasar Zabihullah Mujahid ya tabbatar da cewa Mujib ur Rahman Ansari, limamin masallacin yana cikin wadanda suka mutu.
“Wani malami mai jaruntaka kuma mai jajircewa na kasar ya yi shahada a wani mummunan hari,” in ji shi a shafin Twitter.
Ansari wani malami ne mai fada a ji da ya shahara da zafafan kalamai.
A cikin watan Yuli, yayin wani taron addini a Kabul, ya yi kakkausar suka wajen kare sabbin shugabannin Taliban na Afghanistan.
“Duk wanda ya aikata mafi kankantar aiki a kan gwamnatinmu ta Musulunci, a fille kansa,” in ji shi.
“Wannan tutar (Taliban) ba ta kasance cikin sauki ba, kuma ba za a sauke ta cikin sauki ba.”
Kafin kungiyar Taliban ta koma kan karagar mulki a watan Agustan shekarar da ta gabata, Ansari ya shahara da zagon kasa ga gwamnatocin baya da Amurka ke marawa baya.
Ansari shi ne malami na biyu da ke goyon bayan Taliban da aka kashe a wani harin bam cikin kasa da wata guda, bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai kan Rahimullah Haqqani a makarantarsa ta Kabul.
Haqqani dai ya shahara da yin jawabai na bacin rai ga kungiyar IS, wadda daga baya ta dauki alhakin mutuwarsa.
Ya kuma yi magana kan a bar ‘ya’ya mata su shiga makarantar sakandare, duk da cewa gwamnati ta hana su zuwa karatu a yawancin larduna.
Masallatai da dama a kasar an kai hari a bana,wanda wasu hare-haren kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.
Akalla mutane 21 ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata a ranar 17 ga watan Agusta lokacin da wani bam ya tashi a wani masallaci da ke cike da masallata a birnin Kabul.
IS ta fi kai hari ga tsirarun al’ummomi kamar su ‘Yan Shi’a, Sufaye da Sikhs.
Yayin da IS kungiyar Islama ta Sunni ce irin ta Taliban, su biyun abokan gaba ne kuma suna da sabanin ra’ayi sosai.
Jami’an gwamnati sun yi ikirarin cewa an fatattaki IS amma masana sun ce kungiyar ita ce babban kalubalen tsaro ga masu mulkin Islama a kasar.AFP
A wani labarin kuma, Komai Yayi Wahala A karkashin Mulkin APC – Makarfi
Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya ce rashin tsaro ya tabarbare a karkashin jam’iyyar APP mai mulki.
A wata hira da yayi da BBC Hausa, Makarfi ya ce lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki, rashin tsaro ya kasance a yankin Arewa maso Gabas ne kawai amma duk da haka kasar ta gudanar da zabe saboda matakan da gwamnatin da ke mulki ta dauka a lokacin.